lafiya1910.m4a
|
Likitoci sun yi kashedi da cewa, ciwon bakin ciki ya kan sanya 'ya'ya da iyayensu mata kasancewa cikin hadari. Idan masu juna biyun sun yi saurin jin haushi, kuma ba su ci abinci ko yi barci da kyau ba, zai kawo illa ga zaman rayuwarsu da aikinsu, don haka, dole ne su je ganin likita cikin lokaci, a magance tsanantar ciwon.
Likitoci sun ba da shawarar cewa, iyaye mata da suke sake samun ciki, kuma shekarunsu sun wuce 35 da haihuwa suna fuskantar karin matsin lamba a jiki da kuma zaman rayuwa. Saboda haka, kamata ya yi su kara mai da hankali da kuma kyautata tunaninsu cikin lokaci yayin da suke samun ciki. Har ila yau ya kamata iyalansu su samar da kyakkyawan yanayin jituwa a tsakaninsu. Kana kuma kamata ya yi mijinsu da mambobin iyalansu su nuna masu kauna da goyon baya ta fuskar tunani, a kokarin taimaka musu wajen tafiyar da sabbin sauye-sauye a zaman rayuwa. Haka zalika, ya fi kyau masu juna biyu su ci gaba da aikinsu kamar yadda suke yi a da, su kuma yi mu'amala da sauran mutane, muddin aikinsu ba shi da yawa kuma suna cikin koshin lafiya, lamarin da ya taimaka musu samun farin ciki a duk lokacin samun ciki. (Tasallah Yuan)