in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Batutuwa guda 10 dangane da ciwon sukari (B)
2017-07-24 07:22:40 cri

A shekarun baya, yawan wadanda ke fama da ciwon sukari ya samu saurin karuwa a duk fadin duniya. Duk da haka jama'a ba su san ciwon na sukari sosai ba, suna da rashin fahimta kan wannan ciwo. A makon da ya gabata, na yi karin bayani kan wasu batutuwa dangane da ciwon na sukari. Yau bari in ci gaba da yi muku bayani.

Sakamakon tafiyar lokaci ya sa yawan sukari da ke cikin jinin mutane yake kawo illa ga lafiyar muhimman sassan jikinsu, hakan ya kan haifar da ciwon zuciya, shan inna, jin ciwon a sashen da ke sarrafa sakwanni a kwakwalwa, makanta, yankewar wani sashin jiki, tsayawar koda da dai sauransu. Alal misali, barazanar da masu fama da ciwon sukari suke fuskanta wajen yanke kafaffu ta fi wadanda suke da koshin lafiya yawa har sau 10 zuwa 20.

Kamar yadda kuka sani, akwai nau'o'i guda 2 na ciwon sukari, wato na farko da na biyu. Ba a iya yin rigakafin kamuwa da ciwon sukari na nau'in farko ba. Amma galibi dai nauyin jiki da ya wuce misali da rashin isasshen motsa jiki suna haddasa kamuwa da ciwon sukari nau'i an biyu, saboda haka ana iya yin rigakafi ko kuma hana tsanantar wannan nau'in.n biyu. Abubuwan gaskiya sun shaida cewa, muddin an kyautata zaman rayuwar mutane, alal misali, tabbatar da daidaiton nauyin jiki, motsa jiki a lokaci-lokaci, da cin abinci ta hanyar da ta dace, za su rage barazanar kamuwa da ciwon sukari nau'I na biyu, ko kuma ci gaba da tsanantar ciwon, tare da yin rigakafin bullowar cututtukan da suka biyo bayan kamuwa da ciwon sukari nau'I na biyu.

Masu sauraro, ko kun san ciwon sukari a lokacin samun ciki? Idan masu juna biyu suka kamu da irin wannan ciwon sukari na musamman, yawan sukari da ke jininsu ya fi na masu koshin lafiya, amma bai kai na masu fama da ciwon sukari ba. Irin wadannan masu juna biyu suna fuskantar karin barazanar kamuwa da cututtukan da suka biyo bayan samun ciki. Sa'an nan sun fi fuskantar karin barazanar kamuwa da ciwon suakru na nau'in biyu a nan gaba.

Yanzu haka karin yara sun kamu da ciwon sukari nau'in na biyu, wanda a baya baligai ne kawai suke kamuwa da shi. An bada shawararcewa, cin abinci da yin zaman rayuwa yadda ya kamata suna iya kare yara daga kamuwa da ciwon sukari nau'i na biyu.

Tabbatar da kamuwa da ciwon sukari cikin lokaci yana da matukar muhimmanci ga masu fama da ciwon. In ba a tabbatar da kamuwa da ciwon ko kuma ba a yi jinya cikin lokaci ba, lafiyar masu fama da ciwon kan kara lalacewa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China