in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ilmin ciwon sukari (A)
2017-07-02 10:37:50 cri

A shekarun baya, yawan wadanda suke fama da ciwon sukari ya samu saurin karuwa a duk fadin duniya. Duk da haka jama'a ba su san ciwon na sukari sosai ba, suna da rashin fahimta kan wannan ciwo. A cikin shirinmu na wannan mako da na mako mai zuwa, zan yi bayani kan wasu tambayoyi dangane da ciwon na sukari.

Wasu mutane suna tsammani cewa, ciwon sukari, ba nau'in mummunan ciwo ba ne. A ganinsu, ciwon sukari, wani ciwo ne da yake addabar mutane sannu a hankali, babu bukatar a mai da hankali sosai kan ciwon. To, mene ne gaskiyar lamarin?

Bari in dauki kasar Sin a matsayin misali. Masu nazari na kasar Sin sun kaddamar da sakamakon nazarinsu a mujallar hukumar ilmin likitanci ta kasar Amurka a shekarar 2013, inda suka yi hasashen cewa, masu fama da ciwon sukari da yawansu ya kai misalin kashi 70 cikin dari a kasar Sin ba su san sun kamu da ciwon ba. Sa'an nan, a cikin baligai masu fama da ciwon sukari wadanda suka yi jinya, wasu da yawansu bai wuce kashi 40 cikin dari ba ne suka sarrafa yawan sukari da ke cikin jininsu yadda ya kamata. Jama'a ba su mai da hankali isasshe kan ciwon na sukari ba.

Hakika dai, idan ba a kula cikin lokaci ba, masu fama da ciwon sukari za su makance, ko kuma yanke wani sashin jikinsu, yayin da suke fuskantar babbar barazanar kamuwa da ciwon zuciya, shan inna, ciwon Uraemia, gwargwadon masu koshin lafiya. A shekarar 2012, ciwon sukari ya yi sanadin mutuwar mutane miliyan 1 da dubu 500 a fadin duniya, kana, wasu mutane miliyan 2 da dubu 200 na daban sun rasa rayukansu sakamakon cututtukan zuciya da na magudanar jini da sauran cututtuka, wadanda suka kamu da su saboda yawan sukari da ke jininsu.

Wasu sun yi shelar cewa, ana kamuwa da ciwon sukari ne sakamakon cin abinci ba yadda ya kamata ba, don haka ana iya shawo kan ciwon ta hanyar cin abinci yadda ya kamata, har ma sun ce, wasu nau'o'in abinci suna iya shawo kan ciwon na sukari baki daya.

Akwai nau'o'ikan ciwon sukari guda 2, wato na farko da na biyu. Jikin masu fama da ciwon sukari mai nau'in farko baya iya samar da sinadarin Insulin, kuma ba a iya yin rigakafin kamuwa da shi ba. Masu fama da ciwon sukari mai nau'in biyu kuma jikinsu baya iya amfani da sinadarin Insulin yadda ya kamata, amma ana iya yin rigakafin kamuwa da shi ta hanyar cin abinci da motsa jiki yadda ya kamata. Har wa yau, wajibi ne a yi bincike kan yawan sukari da ke jininsu, da shan magani yadda ya kamata. Duk da haka, ba a iya shawo kansa baki daya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China