in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amfani da wayar salula yayin da ake raka yara na iya lalata nitsuwarsu
2017-06-18 11:21:06 cri

Yanzu wasu iyaye su kan yi wasa da wayar salula da sauran abubuwa yayin da suke raka 'ya'yansu. Wani nazari da aka gudanar a kasar Amurka ya shaida cewa, watakila hakan zai kawo illa ga nitsuwar kananan yara. Ana ganin cewa, nitsuwa za ta iya sa a samu nasara ko a'a.

Masu nazari daga reshen jami'ar Indiana a birnin Bloomington sun bayyana cikin rahotonsu cewa, sun gayyaci wasu kananan yara da shekarunsu suka kai 1 a duniya da kuma iyayensu domin su gwadasu, inda a karo na farko suka gano alakar da ke tsakanin yadda wadanda suke raka kananan yara suke yi da kuma yadda kananan yaran suka dade suna mai da hankali kan wani abu.

A cikin gwajinsu, iyayen da 'ya'yansu dukkansu sun sanya na'urar daukar bidiyo a ka, bayan da masu nazarin suka tantance hotunan bidiyon, sun tabbatar da tsawon lokaci da iyayen da 'ya'yansu suke dauka suna kallon wani abu. Daga baya kuma, masu nazarin sun samar da wasu abubuwan wasan yara,inda suka gayyaci iyayen su raka 'ya'yansu wajen wasa tare. A karshe dai, sun gano cewa, iyayen sun kara mai da hankali kan raka 'ya'yansu tare da sakar musu fusku, kuma yadda 'ya'yansu za su tsawaita lokacin da suke mai da hankali a kan wani abu, nitsuwarsu ta kyautata.

Alal misali, yayin da tsawon lokaci da iyayen da 'ya'yansu suka dauka kallon abu daya a lokaci guda ya wuce dakika 3.6, duk da cewa iyayen sun kalli wani abu na daban, 'ya'yansu za su ci gaba da kallon wannan abun har na Karin dakika 2.3. In an kwatanta da yadda kananan yara da iyayensu su kan kalla.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, a baya, a na daukar nitsuwa a bangaren wani ko wata, a matsayin baiwa, ba a iya sarrafawa. Amma nazarin da aka yi a wannan karo ya shaida cewa, harkokin zamantakewar al'umma su ma za su yi tasiri ko akasin haka ga nitsuwar wani ko wata. A baya, wasu nazarce-nazarce sun tabbatar da cewa, ko kananan yara suna da nitsuwa, ko a'a, wannan ya kasance wata muhimmiyar alamar da ke yin hasashen cewa, ko za su samu nasara a nan gaba ko a'a.

Har ila yau masu nazarin sun yi nuni da cewa, yanzu wayar salula tana samun karbuwa sosai a fadin duniya, wasu iyaye su kan yi wasa da wayar salula yayin da suke raka 'ya'yansu, kila abun da da suka yi zai hana 'ya'yansu su samu nitsuwa yadda ya kamata yayin da suka girma. A maimakon haka, kula da 'ya'yanka tare sake musu fuska, yana iya taimaka musu wajen kyautata nitsuwarsu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China