in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Motsa jiki kullum kan kara barazanar kamuwa da ciwon sankara iri-iri 13
2017-04-16 11:47:01 cri

Kwanan baya, masanan ilmin kimiyya sun ba mu wani dalili na daban na kara motsa jiki! Masana daga hukumar nazarin ciwon sankara ta kasar Amurka sun kaddamar da sakamakon nazarinsu da cewa, watakila kara motsa jiki cikin himma zai iya rage barazanar kamuwa da ciwon sankara iri-iri guda 13, kamar a hanta, a koda, da a mama.

Masanan sun tantance bayanan da ke shafar lafiyar mutane kimanin miliyan 1 da dubu 440 na kasashen Turai da Amurka, wadanda aka dauki shekaru 11 ana gudanar da nazarin a kansu, su kan dauki minti 150 suna motsa jiki, kamar yin yawo, gudu, ninkaya da dai sauransu a ko wane mako, kamar yadda hukumar kiwon lafiya ta Amurka ta shawarta. A lokacin da ake gudanar da nazarin, wasu dubu 187 sun kamu da ciwon sankara.

Masu nazarin sun tanadi ciwon sankara iri-iri guda 26 a cikin nazarinsu. Sakamakon nazarin ya nuna cewa, barazanar kamuwa da ciwon sankara iri 7 da mutanen da su kan motsa jiki kullum suke fuskanta ya ragu da kashi 20 cikin dari, a kalla, idan aka kwatanta su da wadanda ba safai su kan motsa jiki ba. Wadannan ciwon sankara iri 7 su ne ciwon sankara a hanyar abinci tsakanin baki da ciki, hanta, huhu, koda, Cardia, mahaifa da jini.

Barazanar kamuwa da ciwon sankara iri 6 na daban, ita ma ta ragu kadan, wato a bargo, uwar hanji, wuya da kwakwalwa, mara da mama.

Duk da haka, barazanar kamuwa da sauran ciwon sankara iri 13 ba ta ragu sosai ba. Masu nazarin sun yi nuni da cewa, galibi dai, motsa jiki cikin himma da kwazo yana iya rage barazanar kamuwa da ciwon sankara da kashi 7 cikin dari baki daya.

Abin da ya kamata mu lura da shi shi ne, a cikin ciwon sankara iri-iri 13 da ake iya rage barazanar kamuwa da su ta hanyar motsa jiki cikin himma, raguwar barazanar kamuwa da ciwon sankara iri-iri 10 ba ta da nasaba da matsalar kiba, hakan ya nuna cewa, watakila yadda aka rage barazanar kamuwa da su ba shi da nasaba da matsalar kiba. Kana kuma, raguwar barazanar kamuwa da ciwon sankara a huhu tana da nasaba da al'adar shan taba.

Masu nazarin sun yi ce, akwai bukatar kowa ya san cewa, motsa jiki a lokacin hutu yana taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya da mutuwa da wuri, amma nazarin da suka gudanar ya shaida cewa, motsa jiki yana iya rage barazanar kamuwa da ciwon sankara a wasu sassan jiki. Don haka, kamata ya yi masu ilmin liktanci su yayyata cikin himma da kwazo da cewa, motsa jiki yadda ya kamata yana taka muhimmiyar rawa wajen rayuwa ta hanyar da ta dace da kuma yin rigakafin kamuwa da ciwon sankara. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China