lafiya1709.m4a
|
Hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta kaddamar da wani rahoto a kwanan baya, inda a cewarta, kashi 92 cikin 100 na jimillar mutanen duniya baki daya suna rayuwa ne a wuraren da gurbatar iska ta zarce ma'aunin ingancin iska na hukumar WHO.
Hukumar WHO ta yi bincike a kasashe daban-daban na duniya dangane da matsalar gurbatar iska da suke fuskanta,kuma bayanan taurarin dan Adam da tashoshin bincike a kasa sun nuna cewa, tsananin gurbatar iska da yawancin mutanen suke fuskanta a wuraren da suke zaman rayuwa a duniyarmu ya wuce ma'aunin da WHO ta kayyade game da inganci iska ". Ma'aunin da hukumar ta WHO ta tsara shi ne wajibi ne matsakaicin ma'aunin ingancin iska ya kasance maki 2.5 a duk shekara ko kuma kasa da Microgiram 10 na Cubic mita 1. PM 2.5 su ne kananan abubuwan da fadinsu bai wuce Micromita 2.5 ba.
Madam Maria Neira, wata jami'ar WHO mai kula da harkokin kiwon lafiyar al'umma da muhalli ta yi bayanin cewa, sabon binciken yana taimakawa wajen kimanta yawan mutane fiye da miliyan 6 da suka rasa rayukansu sakamakon gurbatar iska a cikin gari da kuma wajen daki.
Alkaluman hukumar WHO ya nuna cewa, matsakaicin ingancin iska na maki 2.5 da ake samu a birane da yankunan karkara a kasar Sin ya kai Microgiram 54 na Cubic mita 1. A duk lokacin da aka ambaci biranen kasar Sin, ana maganar wuraren da ake fama da mummunan gurbatar iska, inda ake samun Microgiram 59 na Cubic mita 1 a cikin maki 2.5 na ma'aunin ingancin iska na biranen.
Rahoton da hukumar ta WHO ta kaddamar ya yi karin bayani da cewa, zirga-zirgar motoci, jiragen kasa, jiragen sama da dai sauransu, yin amfani da makamashi a gida, kona shara, samar da wutar lantarki ta hanyar kona kwal, da harkokin masana'antu da dai makamantansu su kan gurbata iska. Don haka, hukumar ta WHO ta ba da shawarar cewa, kamata ya yi gamayyar kasashen duniya su gaggauta daukar matakai wajen yaki da gurbatar muhalli. To, yaya za a magance matsalar gurbatar iska? Alal misali, yayata hanyar zirga-zirga maras gurbatar muhalli a birni, kamar hawan keke a maimakon tuka mota, sarrafa shara mai kwari yadda ya kamata, yayata yin amfani da makamashi da murhu maras gurbata muhalli a gida, yin amfani da makamashi da ake iya sabuntawa, da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli yayin da ake gudanar da harkokin masana'antu. (Tasallah Yuan)