lafiya1706.m4a
|
A baya wasu suna ganin cewa, yadda mata suke aikin dare a kullum, ya kan hana agogon kwakwalwarsu ya yi aiki yadda ya kamata, lamarin da watakila zai kara musu barazanar kamuwa da ciwon sankarar mama. Amma kwanan baya, jami'ar Oxford ta kasar Birtaniya ta kaddamar da sakamakon nazari da ta gabatar, wanda ya nuna cewa sababbin shaidu sun nuna cewa, yin aikin dare ba ya kawo illa ga lafiyar mata kamar yadda ake zato a baya.
Hukumar nazarin ciwon sankara ta duniya, karkarshin shugabancin hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO, ta kaddamar da sakamakon nazarinta a shekarar 2007, inda ta ce, kila yin aikin dare zai haddasa kamuwa da ciwon sankara. Amma jami'ar Oxford ta yi bayani da cewa, hukumar nazarin ciwon sankara ta duniya ta gudanar da binciken ne kan dabbobi kawai. A wancan lokaci, babu isassun abubuwan shaida dangane da mu Bil Adama.
Don haka masu nazarin daga jami'ar Oxford suka tantance bayanan da suka samu daga manyan bincike guda 3, wadanda suka shafi 'yan Birtaniya mata dubu 800. Amma ba su gano wasu shaidu da ke nuna alakar da ke tsakanin yin aikin dare, da kuma karuwar barazanar kamuwa da ciwon sankarar mama ba.
Masu nazarin sun kuma hada bayanansu da kuma bayanan da aka samu daga kasashen Amurka, da Sin, da Sweden da Holland, sun kuma tantance su duka. A cikin wadannan mata miliyan 1 da dubu 400 da aka yi musu binciken, masu fama da ciwon sankarar mama su 4660 ne kawai suka taba yin aikin dare.
Bayan haka kuma, masu nazarin sun bambanta barazanar kamuwa da ciwon sankara a mama, tsakanin matan da suka dauki dogon lokaci suna aikin dare, da kuma matan da ba su taba yin aikin dare ba. Binciken na su ya nuna cewa lallai babu wani bambanci sosai. Don haka masu nazarin suka ce, yin aikin dare a lokaci-lokaci, ko kuma yin aikin dare cikin dogon lokaci, ba za su kara wa mata barazanar kamuwa da ciwon sankara a mama ba.
Hukumar kula da lafiyar ma'aikata da tsaro ta Birtaniya, ta ba da kudin tallafi kan wannan nazari. Babban mashawarcin hukumar ta fuskar ilmin kimiyya ya bayyana cewa, ko da yake sakamakon nazarin ya nuna mana cewa, yin aikin dare ba zai kara wa mata barazanar kamuwa da ciwon sankara a mama ba, duk da haka kamata ya yi shugabanni su mai da hankali kan sauran abubuwan da suke haifar da barazana sakamakon yin aikin dare, a kokarin kara tabbatar da lafiyar ma'aikata da kuma tsaronsu. (Tasallah Yuan)