Tare da fatan daukacin ma'aikatan ku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake a nan birnin Kano. A daidai wannan rana ta Asabar 3 ga watan Disamba, 2016 wanda ake gudanar da shagulgulan biki domin tunawa da kafuwar gidan rediyon kasar Sin CRI shekaru 75 masu albarka, wato daga shekarar 1941 zuwa 2016. Lalle ya dace a yaba wa tashar CRI bisa namijin kokarin yin aiki tukuru cikin shekaru 75 wajen fadakar da al'ummar duniya hakikanin abubuwan dake faruwa a kasar Sin, al'adun Sinawa masu ban sha'awa da kuma sanar da masu sauraro halin da duniya ke ciki.
Ina fatan gidan rediyon kasar Sin zai ci gaba da samun farin jini da karbuwa wajen al'ummar duniya. Ina kuma fatan sashen Hausa na CRI zai kara samun daukaka tsakanin daukacin harsuna 65 da gidan rediyon CRI ke watsa shirye shiryensa da su. Lalle ya dace a jinjina wa ma'aikatan CRI baki daya, domin bisa gudunmawar su da jajircewar su ne CRI ya cimma wadannan nasarori cikin shekaru 75 da suka gabata. Na gode.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Shugaban kungiyar
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria