lafiya1634.m4a
|
Kiba, matsala ce da ke matukar illa ga lafiyar jikin dan-Adam. Wani nazari da aka gudanar a kasar Birtaniya ya gano cewa, Kiba wadda ke haddasa nauyi fiye da kima, tana kara wa dan Adam barazanar kamuwa da na'u'o'in cutar sankara guda 10.
A kwanakin baya ne masu nazari daga kwalejin ilmin kiwon lafiya da cututtuka a yankuna masu zafi na London da wasu hukumomi suka kaddamar da rahoton nazarinsu, inda suka tattara bayanai na binciken lafiyar 'yan Birtaniya miliyan 5 da dubu 240 da suka gudanar wadanda shekarunsu suka wuce 16 a duniya, sun kuma dauki matsakaicin shekaru 7 da rabi suna gudanar da wannan bincike. A lokacin da aka fara wannan nazarin, wadannan 'yan Birtaniya miliyan 5 da dubu 240 ba su kamu da cutar sankara ba, amma a yayin da ake gudanar da nazarin, dubu 167 daga cikinsu sun kamu da cutar sankara iri-iri guda 22 da aka saba kamuwa da su. Masu nazarin sun mai da hankali kan nazarin alakar da ke tsakanin barazanar kamuwa da cutar sankara da kuma mizanin BMI na ma'aunin nauyin mutum, tare da yin la'akari da jinsinsu, shekarunsu a duniya, al'darsu ta shan taba da yanayin zamantakewar al'ummar kasa da fuskar tattalin arziki. Mizanin BMI, mizani ne na ma'aunin nauyin mutum bisa kilogiram. Idan mizanin nauyin mutum ya wuce Kilogram 25, to, nauyin mutum ya wuce misali, yayin da idan ya wuce 30, mutumin ya shiga sahun masu kiba.
Masu nazarin sun gano cewa, barazanar kamuwa da nau'o'in cutar sankara guda 10 yana da nasaba da mizanin ma'aunin nauyinsa. Idan mizanin ya karu da maki 5, to, barazanar kamuwa da cutar sankarar mahaifa, madaciya, da koda ta karu da 62%, 31% da 25%, kana da barazanar kamuwa da cutar sankara a jijiyar da ke sarrafa sinadaren da ke daidaita bugun zuciya da jinni. Cutar sankarar hanta, uwar hanji, kwan mace da mama ta kan karu sakamakon matsalar kiba da kuma nauyin da ya wuce misali.
A cewar masu nazarin, yanzu haka yawan wadanda suke fama da matsalar kiba da wadanda nauyinsu ya wuce misali yana saurin karuwa a duk fadin duniya. Sanin kowa ne cewa, lamarin ya haifar da karuwar masu cutar sukari da masu ciwon zuciya. Amma wannan nazari da aka yi a kasar Birtaniya ya shaida mana cewa, idan lamarin ya ci gaba da karuwa, watakila yawan masu fama da cutar sankara zai karu sosai a duniyarmu baki daya. (Tasallah Yuan)