in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shan taba sigari ga masu juna biyu yana kara wa 'ya'yansu mata barazanar kamuwa da cutar sankara
2016-10-17 10:31:23 cri

A kwanan baya ne jami'ar kasar Australiya ta kaddamar da wani sakamakon sabon nazari, wanda ke bayyana cewa, matan da suke shan taba sigari a yayin da suke da ciki, akwai yiwuwar 'ya'ya mata da za su haifa za su fuskanci barazanar kamuwa da cutar sankara da kuma mama bayan da suka girma.

Masu nazarin sun wallafa rahoton nazarin nasu ne a cikin mujallar nan mai suna "haihuwar bil Adama" ta kasar Birtaniya da cewa, sun samu bayanan da suka shafi mata 1500 daga cikin binciken da hukumomin lafiya na kasar Australiya suka gudanar. Bayan da masu nazarin suka tantance bayanan, sun gano cewa, yayin da wadannan mata 1500 suke a matsayin 'yan tayi a cikin mahaifansu, idan mahaifansu mata suka rika shan taba ba tare da kasala ba, to, akwai yiwuwar wadannan mata 1500 su fara al'ada tun kafin lokaci, lamarin da ya sanya su kara fitar da kwai sau da dama a duk tsawon rayuwarsu, hakan na iya sanya su saurin kamuwa da cutar sankara a sassan jikinsu masu nasaba da haihuwa sakamakon kara samun sinadarin Hormone na mata fiye da kima.

Masu nazarin na kasar Australiya sun bayyana cewa, sun kara gano cewa, kafin a haife mu 'yan Adam, galibi dai an tabbatar da yanayin jikinmu a fannoni da dama, har ma da dabi'armu. Suna kuma ganin cewa, illolin da shan taba da sauran munanan dabi'u suka haddasawa masu juna biyu su ma suna kawo illa ga lafiyar 'ya'yansu cikin dogon lokaci.

A baya, wasu nazarce-nazarce sun shaida mana cewa, shan taba a yayin da mata suke da ciki yana da nasaba da barazana da dama da 'ya'yansu suke fuskanta, kamar rashin nauyin jarirai sabbin haihuwa, rashin karfin huhun jarirai sabbin haihuwa, kananan yara su kan yi fama da ,atsalar cutar numfashi ko asma da matsalar rashin kiba. Sakamakon nazari da masu nazarin na kasar Australiya suka samu ya shaida mana sabuwar illar da masu juna biyu suka fuskanta sakamakon shan taba sigari, lamarin da ya samar da ya tabbatar da shaidun gudanar da nazarce-nazarce a wannan fanni. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China