in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cin abinci a gaban madubi yana iya kara kamshin abincinka
2016-09-19 08:39:21 cri

Mene ne bambancin mutum ya ci abinci shi kadai da kuma cin abinci tare da wasu mutane? Masu nazari daga kasar Japan sun amsa cewa, a duk lokacin da aka ci abinci cikin taron jama'a, hakan na taimakawa wajen kara jin dadin dandanon abinci, duk da cewa, cin abinci a gaban madubi na iya sa a kara cin abinci.

A kwankin baya ne dai masu nazari daga jami'ar Nagoya dake kasar Japan suka kddamar da rahoton nazari nasu, inda a cewarsa, sun gayyaci dalibai 16 masu matsakaicin shekaru 21da rabi a duniya da kuma tsoffafi 16 da matsakaicin shekarunsu suka kai kimanin 68 a duniya, da su dandana tasasshiyar shinkafa mai gishiri da kuma mai zaki a gaban madubi da kuma inda babu madubi a gabansu. A ko wane lokaci sun dauki dakikoki 90 wajen dandana shinkafar, daga baya kuma sun dauki mintoci da dama kafin su dandana shinkafar, daga bisa ni kuma sai suka sake dandana shinkafar.

Bayan da wadannan dalibai da tsoffafi suka dandana wannan shinkafa a ko wane lokaci, sai nan da nan masu nazarin sun tambaye su ko shinkafar tana da dadi ko a'a? Ko suna son sake dandanawa? Mene ne ra'ayoyinsu bayan da suka dandana? Masu nazarin sun tantance amsoshinsu, inda suka gano cewa, dukkan dalibai da tsoffafin suna ganin cewa, idan suna dandana shinkafar a gaban madubi, sun fi jin dadin dandanon abun da suka ci, kuma suna son sake dandanawa, wannan ya sa suke cin shinkafar da yawa.

Haka kuma, wadannan dalibai da tsoffafi ba su iya bambanta tafasasshiyar shinkafa mai gishiri da kuma mai zaki ba duk da cewa, akwai madubi a gabansu ko kuma babu. Masu nazarin sun kuma kimanta yanayin sha'awa da jin dadi da wadannan dalibai da tsoffafi suka nuna yayin da suke dandana shinkafar, sun kuma gano cewa, kasancewar akwai wanin madubi a gabansu ko kuma babu, ba zai yi tasiri kan halayyar da suka nuna ba.

Masu nazarin suna ganin cewa, yanyin da mutum yake ciki yayin da yake cin abinci ya kan yi tasiri kan ra'ayinsa dangane da ko abincin yana da dadi ko a'a. Duk da cewa,mutum ya ci abinci shi kadai ne, amma cin abinci tare da jama'a ya fi sa a kara jin dadin abincin. Cin abinci a gaban madubi yana kwaikwayon yadda ake cin abinci tare da jama'a, lamarin da ya sanya mutane su kara jin dadin abincin da suke ci.

A shekarun baya, matsalar karuwar yawan tsoffafi tana kara adabar kasar Japan, inda karin tsoffafi suke cin abinci su kadai, lamarin da watakila ya sa ba sa sha'awar cin abinci, ta yadda za su yi fama da matsalar karancin abubuwa masu gina jiki. Masu nazarin na Japan sun yi hasashen cewa, nazarin da suka gudanar zai taimakawa tsoffafin da sauran mutane su kara jin dadin cin abinci da kuma kyautata zaman rayuwarsu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China