Waiwaye adon tafiya, ina iya tunawa da lokacin da na fara sauraren Radio Cri a shekarar 1979 kuma tun a wancan lokacin ne nake samun labaru da rahotanni game da hakikanin irin wainar da ake toyawa a sabuwar kasar Sin ta zamani da kuma duniya baki daya. A zahirin gaskiya, cri ya taimaka sosai wajen fadakar da al'ummar ketare labaru da rahotanni sahihai wayanda ke karin haske a dangane da kasar Sin da duniya. Zuwa yanzu da ake gudanar da bukukuwan murnar cikon shekaru 75 da kafuwar Radio Cri, muna iya cewa, gidan radiyan Cri ya samu ci gaba da sauye-sauye masu inganci irin na zamani inda gidan Radiyon ke watsa shirye-shiryensa ta kafufin sadarwa na zamani wato ta facebook, twitter, whats'up da kuma ta akwati mai photo da dai sauransu. A zamanin yau, cri yana samun galaba wajen aiwatar da shirye-shiryensa ga duniyar masu sauraro. Kana Cri a cikin shekaru 75 da kafuwarsa cri da ma'aikatansa sun sada zumunci da masu saurarensu a fadin duniya kuma da yawa daga cikin masu sauraren cri sun samu damar kawo ziyara a kasar Sin dan kara wayin kai ga masu sauraro da kuma kara sada zumunci. A shekarar 2013, cri English sun shirya gasar kacici-kacici mai suna 'feeling Beijing' inda wanda ya samu nasara ya ziyarci kasar Sin yayinda sauran harsunan Spanish, Frenci, Portugese da dai sauran suka gaiyaci mutane 10. Hakika cr ya yi kokari sosai wajen gudanar da aiyukansa a fadin duniya. Muna fata gidan Radiyon cri da ma'aikatansa za su kara yin kwazo da himma kamar yadda suka yi a cikin shekaru 75. Su ma cri Hausa sun yi kokari sosai wajen fadakar da al'ummar duniya game da kasar Sin da duniya kana kuma sun taimaka sosai wajen daga martaba da kimar gidan Radiyon cri a dud duniyar masu sauraro. A cikin shekaru 52-53 da kafuwar cri Hausa, masu sauraro da yawa sun samu ilmi da wayin kai game da kasar Sin da jama'arta da ma dud duniya.
Muna fatan za ku kammala bukukuwa lafiya, amin.
Daga Malam Ali Buuge kiraji Gashua, jihar Yobe, taraiyar Nigeria.