Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri da fatan daukacin ma'aikatan ku suna nan kalau a birnin Beijing kamar yadda nake lafiya kalau.
Bayan haka, ina farin cikin shaida muku cewa, yau Laraba 1 ga watan Yuni na ji dadin sauraron sabon shirin ku na 'Gani Ya Kori Ji' wanda malamai suka tattauna alfanu da kuma illolin hanyoyin sadarwa na zamani.
Hakika idan aka yi la'akari da irin gagarumar gudunmawar da hanyoyin sadarwa na zamani ke bayarwa ga rayuwar mu ta yau da kullum za a iya cewa san-barka , sakamkon yadda ake iya aikewa da dimbin sakonni cikin kiftawar ido zuwa kowanne loko da sako na fadin duniyar nan. A halin yanzu, amfanin hanyoyin sadarwa na zamani ya zarce batun aikewa da sakonni, wato ya kai wani matsayi da kusan za a iya cewa babu wata mu'amala da babu sadarwa ta zamani a ciki, tun daga harkokin ciniki da kasuwanci, bincike da neman ilimi, sufuri, biyan kudaden hidima da sauran hada hadar kudi. Yanzu kowa ya gamsu cewa, hanyoyin sadarwa na zamani sun ba da gudunmawa mai yawa tare da kawo saukin gudanar da al'amuran yau da kullum.
Ba shakka, ya zama wajibi a yabawa masana da suka kirkiro fusahar sadarwa ta zamani. Idan zan ba da misali da ni kaina, a shekarun 1990 ba na iya aikowa da sashen Hausa na CRI sakonni masu yawa kamar a yanzu inda nake iya aiko sa sakonni da dama akai akai ta hanyar e-mail. Wannan ya kara karfafa zumuncin da ke tsakani na da sashen Hausa.
Sai dai wani abin takaici, a daidai wannan lokaci da ake kan cin moriyar hanyoyin sadarwa na zamani, an fara cin karo da matsalar masu yin kutse cikin shafukan yanar gizo na mutane ko hukumomi inda suke satar bayanai ko kuma aikata zamba. Koda yake, kasashe da dama sun dauki gabarar yaki da wannan matsala bisa la'akari da barazanar da matsalar ke yi ga muhimman bayanai mallakar hukumomi da daidaikun mutane.
Dangane da haka, ya zama wajibi a yabawa kasar Sin kasancewa tana daga cikin kasashe da ke kan gaba wajen yaki da matsalar kutsen yanar gizo a duniya bisa la'akari da yadda kasar Sin ta shigar da batun cikin ajandar taruka biyu na majalisun NPC da CPPCC da aka gudanar a watan Maris da ya gabata. Ina fatan kasashen duniya za su hada kai wajen yakar wannan matsala ta kutsen shafukan yanar gizo da ke zama babbar barazana ga harkokin sadarwa na zamani.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Shugaban kungiyar
Great Wall CRI Listeners Club
Kanon Dabo, Nigeria