Bayan gaisuwa mai tarin yawa dafatan dukkanin ma'aikatan sashen Hausa suna lafiya.
Bayan haka nakasance mai farin cikin jin wannan shiri dukda bawannanne karo na farko dajin labarin Malam Sani Alasan da matarsa Halima da diyarsu Aisha da Hauwa'u, naji dadin jin wannan shiri, domin a matsayina na ma'abocin soyayya na gamsu da jinjina musu saboda dukda bambamcen al'ada, rayuwa sun aminta da juna, kuma kamar sun shiga zuciyata domin na yarda da cewar soyayya ba ruwanta da kabila, kasa ko kalar fata, domin koni da kaina a matsayina na matashi wanda bayi aureba inaga zan iya aure daga kowane kabila a duniya indai akwai soyayya, don haka watakila wata basiniyace amaryartawa,. Atakaice labarin Malam Sani ya kuma tabbatar da cewa a duk inda kasami kanka to Allah zai iya samar maka da abokiyar zama, kuma ya nuna juriya da amintaka sosai. Ina mai godiya ta musammam a mamadina da duk 'yan kungiyar Great Wall a Kanon Dabo game da wannan shiri na musammam da kuka gabatar akan Hausawa a kasar Sin domin ya kuma ilimantar da dimbin masu sauraro akan karamci da amintakar al'ummar Sinawa ga baki 'yan kasashen waje, wadda wasu daga cikin masu sun yanke in sun sami dama zasuzo kasar Sin musammam birnin Guonzhou. Banda haka ina fatan inkun sami dama zaku gabatar da shiri mai suna 'Sinawa a Kasar Hausa' ko 'Sinawa a Najeriya ko Afirka' domin a gabatar da bayanai akan yadda sinawa suke tafi da rayuwarsu, mudai nan a Kanon Dabo sai muce san barka, domin Sinawa suna tafi da rayuwarsu lafiya ba tsangama sannan suna gabatar da ayyuka na bunkasa garinmu da cigaban al'umma, nagode.
Wassalam, Abdulkadir Ibrahim Great Wall C.L.C Kano, Nigeria.