Slm. Zuwa ga malama Fatimah Liu, jagorar hulda da masu sauraro, cri Hausa.
Hausawa suna cewa, "ko kana da kyau, ka kara da wanka". Agaskiya kuna kokari sosai wajen kawo mana labaru da rahotanni masu dumi-dumi kuma akan lokaci. Amma dud da haka, ina mai baku wata shawara cewa, ku dunga yawaita sabunta labaru da rahotannin da kuke kawo mana a shafinku na Hausa.cri.cn, domun sau da yawa kuna barin wasu rahotanni da labaru da suka zama kwantai. Kamata ya yi ku kara azama kamar yadda takwarorinku na cri English suke yi. Yin hakan zai taimaka wa mu masu sauraro wajen samun labarai da rahotanni da suka jibanci kasar Sin da ma dud duniya baki daya.
Kana muna kara mika godiyarmu ga dukkan ma'aikatan sashin Hausa na Radio kasar Sin, bisa kokarinku na wayar mana da kai adangane da harkokin siyasar kasar Sin da kuma alakar kasar Sin da kasashenmu na Afirka masu tasowa da ma harkokin siyasar Duniya.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.