in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin kasar Sin da Najeriya
2016-04-01 08:43:51 cri
Zuwa ga Malama Fatima Liu sashen Hausa na CRI,

Bayan gaisuwa mai yawa dafatan dukkanin ma'aikatanku suna lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake a birnin Kanon Dabo.

Bayan haka naji dadi da farin ciki akan taron da aka gabatar ranar 30/03/2016 a birnin Abuja Nigeria, kan hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin kasar Sin da Najeriya. A gaskiya kasidu na bayanai na irin nasatori da aka samu a wannan fanni naji dadinsu, tabbas akwai dimbin nasarori da aka samu a wannan fanni musammam mu dake nan Najeriya mun shaida, musammam jahar Kanon Dabo munga yadda sinawa suka bunkasa mana gari ta kowane fanni in aka dubi fannin tattalin arziki, kanfanonin Sinawa suna bada gudunmawa ta fannin samar da aikinyi da kayan masarufi na yau da kullum, banda 'yan Najeriya suma da suke gabatar da rayuwarsu a Kasar Sin suna kuma samun bunkasuwa. Anan in aka duba za'a akwai bunkasuwa ta fannin tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Sinawa da 'yan Najeriya. Banda haka ina murnar shirin da kukeson gabatarwa a tashar NTA kan dalibai akasar Sin, tabbas wannan shiri zai kuma jawa hanakalin mutane da kara samusu san sha'awar kasar Sin. Inai maiku fatan alheri. Nagode.

Wassalam, Abdulkadir Ibrahim. Great Wall CRI listeners club, Kano.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China