Buba shakka sabbin shugabannin kasar Sin sun kai matsayin koli a dud duniya wajen girbe dabi'ar cin hanci da karbar rashawa a kasar sin tare da sa kaimi ga aiwatar da yin kywaskwarima da kyautata jin dadin zaman rayuwar al'ummar sinawa ta hanyar samar da moriya ga jama'ar kasar Sin. Tun a shekarar 2013 da sabbin shugabannin jamhuriyar jama'ar Sin da suka dare madafin ikon mulkin kasar Sin suka daura damarar yaki da cin hanci da karbar rashawa a kasar Sin suka cimma manyan nasarori masu yawa ta fannin yaki da cin hanci inda suka samu nasarar aiwatar da hukunci a kan Bo Xilai wanda wata matsakaiciyar kotun al'umma(intermediate people's court) wanda ke zama a lardin Shandon na kasar Sin suka tuhuma kuma suka kama Bo Xilai da laifukan cin hanci da kuma amfani da matsayinsa ta hanyar da bata dace ba. Banda Bo Xilai ma, gwamnatin kasar Sin ta yi nasarar bankadowa tare da aiwatar da hukunci ga wasu sinawa da aka kama da laifin cin hanci a kasar Sin, lamarin da ya kara fito da tagomashin kasar Sin a dud duniya. Bisa wannan kyakkyawar aniya ta kasar Sin, ina fata gwamnatin kasar Sin za su taimaka wa sabuwar gwamnatin madugun canji Gen. Muhammadu Buhari wajen murkushe dabi'ar cin hanci da karbar rashawa wadda ta yi wa harkokin gudanarwar mulkin gwamnatin Nigeria dabaibayi, ganin kasar Sin ta yi wa sauran kasashe takwarorinta fintinkau da zarra wajen kawar da cin hanci da karbar rashawa. Dole ne, kasashen duniya su hanzarta yin da sabbin shugabannin kasar Sin karkashin jagorancin shugaban kasar Sin mr. Xi Jinping bisa dagewa wajen kakkabe tarnakin cin hanci dake neman yin muguwar illa ga bunkasuwar kasar Sin ta zamani.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, Nijeriya