Gabannin ranakun zabukan gama-gari wanda aka gudanar a ranar asabar 28 ga watan Maris na 2015 a Nigeria, sashin Hausa na Radio kasar Sin kun yi kokari sosai wajen sanar da dud duniya yadda yan Nigeria suke gudanar da zabuka da sauran lamura da suka jibanci harkokin zabe a taraiyar Nigeria. Babu shakka da yawa daga cikin masu sauraro sun nuna yabonsu ga cri Hausa bisa maida hankali da kuka yi ga sha'anin zabe a Nigeria. Muna fata kasashen Sin da taraiyar Nigeria za su kara fadada kyakkyawar huldar amunci da musayar al'adu da hadin gwiwa da samun ci gaba ta fannin huldar diplomasiyya da kyautata zaman moriyar juna bisa manyan tsare-tsare da dai sauransu. Kimanin fiye da shekaru 40 da fara huldar diplomasiyya da abokanta da cin moriyar juna tsakanin Nigeria da jamhuriyar jama'ar Sin, lamarin daya kawo wa kasashen 2 babbar moriya mai yawa.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.