Likitoci na Canada sun gabatar da wani rahoto a cikin mujallar kimiyya ta kasar Birtaniya a kwanan baya, inda suka bayyana cewa, sun yi bincike da nazari kan alakar da ke tsakanin wurin aiki da kuma yawan mutanen da suka kamu da ciwon sukari, wadanda shekarunsu suka kai 35 a duniya, amma ba su kai 60 a duniya ba, inda suka yi nazari tare da gudanar da bincike kan adadin da suka shafi lafiyar mutane 7443 mazauna unguwoyin Canada daga shekara ta 2000 zuwa ta 2001.
Masu nazarin sun gano cewa, babban matsin lambar da mata suke fuskanta ta fuskar aiki yana da nasaba da karuwar barazanar kamuwa da ciwon sukari da suke fuskanta, amma babu irin wannan alaka a tsakanin matsin lambar da maza suke fuskanta da kuma karuwar barazanarsu ta kamuwa da ciwon sukari. Ko da yake ya zuwa yanzu ba a san aihinin dalilin da ya sa haka ba, amma akwai bukatar ci gaba da yin nazari a kan lamarin, amma masu nazarin suna ganin cewa, akwai wasu dalilan da suka haddasa hakan. Alal misali, a yayin da suke fuskantar matsin lamba, maza da mata sun sha bamban kwarai da gaske wajen tinkarar wannan matsala a bangaren jiki da kuma tunani. Haka kuma, sinadarin Hormone da ke jikin mata ya sha bamban sosai da wanda ke jikin maza, hakan ya sa nan da nan irin aikace-aikacen da matan kan yi ya kan yi illa ga lafiyarsu sakamakon irin wannan matsin lamba, alal misali, su kan ci kayayyakin abinci masu maiko sosai da kuma zaki, a kokarin rage bakin ciki da ke cikin zuciyarsu.
A duk lokacin da ma'aikatan kamfani suka kara samun sassauci da 'yancin yanke shawara, suna iya kara ba da jagora a yayin da suke gudanar da ayyukansu, to, hakan zai sa su kara gamsuwa da ayyukansu, kuma matsin lambar da suke fuskanta a wajen ayyuka zai ragu, kana za su kara yin ayyuka yadda ya kamata. Saboda haka masu nazarin sun bai wa masu daukar ma'aikata shawarar sake yin la'akari da cewa, ko ana mai da hankali kan kananan abubuwa fiye da kima yayin da yake taimakawa ma'aikatan wajen gudanar da ayyukansu.(Tasallah)