Ina mai matuka mika godiyarmu ga sashen hausa na cri a kan kokarinsu na sanar da mu abin da ba mu sani ba, wanda ya shafi illimantar da mu ta fannoni daban daban kamarsu a'ladu addinai zamantakewa, da dai makamantansu, ba shakka shirinku na ALLAH DAYA GARI BAMBAN na ranar juma'a ya kara muna fahimta tare da sani irin rawar da kananan kabilun kasar sin ke takawa ga ci gaban kasa tare da yadda kasar sin ke bayar da muhimmanci ga kananan kabilun kasar sin komi kan kantarsu tare da ba su muhinmanci sabani wadansu kasashe da ba su la'akari da kabilunsu,, ba shakka wannan ya nuna muna karara da cewa kwamitin tsakiya na kasar sin yana ba da muhimiyar kulawa ga kabilun kasar sin manya da kanana baki daya,wanda shi ke kawo fahimtar juna tare da son juna da zamowar al'ummar kasa su zamo tsintsiya madaurinki daya tare da ci gaban kasa baki daya, fatata a nan shi ne ya kamata shugabanninmu na Afrika da su yi kokarin koyi da kasar sin ta zamani ko da za mu sami ci gaba tare da fahimtar juna a kasashenmu na afrika baki daya. Nagode daga mai sauraronku a ko da yaushe.
Bello Abubakar Malam Gero Sokoto Nigeria.