in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bunkasuwar sabuwar kasar Sin ta zamani
2013-12-18 09:37:35 cri

A ranar alhamis 10 ga watan Disamban da muke ciki shekara ta 2013 mai karewa, na maida hankali adangane da taron kwamitin tsakiya na jam'iyar kwaminist ta Sin. A yayin taron da shugabannin kasar Sin suka gabatar da jawabai, na kara samun ilmi da fahimta ta zahiri mai karko adangane da muhimman shirye-shiryen da gwamnatin kasar Sin ke aiwatarwa ta fannin raya bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin tare da daukan muhimmanci ga kara samar da yalwatuwar rayuwa ga Sinawa da dai sauran batutuwa masu ban sha'awa ainun. Hakika bayanan da shugaban kasar Sin Mr. Xi da mataimakinsa suka gabatar ya burgeni kuma hakan zai taimakawa ainun wajen kara daura kasar Sin a wasu saban ci gaba mai ma'ana ga samun bunkasuwa mai yawan mai inganci. Kazalika, na gamsu da batutuwa 6 da gwamnatin kasar Sin ke da aniyar daura muhimmanci akai a nan kadan cikin sabuwar shekara ta 2014 wadda ke gaba da zuwa. Banda wannan kuma, na kara samun gamsuwa a bisa kyakkyawan shirin yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen ketara masamman ma kasashenmu na Afirka masu tasowa da zummar ingiza ci gaban bunkasuwar kasar Sin da kasashen duniya. Wannan kudirorin gwamnatin Sin su 6, sun burgeni yadda yakamata inda taron nuna muhimmanci ga maida hankali akan wannan batutuwa 6 da suka hada da: kyautata tsarin masana'antu, kula da matsalar basussuka, sa kaimi ga raya yankunan kasar Sin cikin daidaito, bada tabbaci da kyautata rayuwar jama'a, kara bude kofa ga kasashen waje, bada tabbaci ga ingancin abunci. Anan, ina kara yaba wa gwamnatin tsakiya ta kasar Sin nagartattun matakai da suke dauka wajen ingiza ci gaban tattalin arzikin Sin mai tasiri ga Sin dama dud duniya.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China