Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri, da fatan baki dayan ma'aikatanku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, na saurari shirinku na 'Allah daya gari bamban' na jiya Jumu'a 13 ga wata, wanda Malamai Danladi (Jin) da Mamman Ada suka gabatar mana.
Hakika, wannan shiri ya burge ni matuka sakamakon yadda ya nuna irin walwala ta 'yancin bin addini da ta bin salon al'adar kabilar ta Yigu, sakamakon manufofi na gatanci ga kananan kabilun kasar Sin da gwamnatin tsakiya ta bullo da su tun bayan kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949. Ba shakka, bayan da na saurari wannan shiri, na ji dadi sosai kuma na kara yaba wa manufofin gwamnati dake kare kananan kabilu tare da al'adunsu, musamman idan an yi la'akari da cewa yawan al'ummar wannan kabila ta Yigu bai taka kara ya karya ba idan an kwatanta yawansu da na kabilar Han mafi rinjayen dake da kashi 92% cikin dari, amma duk da haka gwamnati na kulawa dasu.
Wannan ko shakka babu, yana da matukar tasiri ga bunkasa al'adu na kananan kabilun kasar Sin, inda hakan zai yi tasiri wajen rayawa tare da bunkasa al'adun Sinawa baki daya. Ko a kwanakin baya, na karanta wani labari a shafin yanar gizon sashen Inglishi na CRI dake magana kan kauyen Yakou dake lardin Yunnan. Inda a nan ma gwamnatin matakin karamar hukuma ke karfafa gwiwar kananan kabilu wajen ci gaba da riko da al'adunsu na gargajiya musamman nacewa ga al'adar nan ta yi wa gidajensu ado irin na gargajiyar kauyen. Har ma a wani bangare na zaburar da mutanen kauyen wajen yin riko da al'adunsu, gwamnatin karamar hukumar kan bayar da kudin tallafi na Yuan 300 kowanne wata ga mutumin dake raya daya daga cikin al'adun kauyen. Lalle, wannan labari ya burge ni, kuma na gamsu da kokarin gwamnati na raya al'adun gargajiya. Na gode.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria