in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar ANC ta cimma nasarar babban zaben kasar Afirka ta Kudu
2019-05-12 16:59:55 cri
Hukumar zaben kasar Afirka ta Kudu ta gabatar da sakamakon babban zaben kasar a jiya, inda aka shaida cewa, jam'iyyar dake kan karagar mulkin kasar wato ANC ta cimma nasarar zaben kasar na shekarar 2019.

Bisa sakamakon zaben, yawan kuri'un da jam'iyyar ANC ta samu ya kai kashi 57.51 cikin dari, yawan kuri'un da jam'iyyar adawa wato DA ta samu ya kai kashi 20.76 cikin dari, kana yawan kuri'un da jam'iyyar EFF ta samu ya kai kashi 10.79 cikin dari. Bisa wannan sakamako, jam'iyyar ANC za ta samu kujeru 230 a cikin dukkan kujeru 400 na majalisar dokokin jama'ar kasar, jam'iyyar DA za ta samu kujeru 84, da kuma jam'iyyar EFF za ta samu kujeru 44. Kana sauran jam'iyyu 11 za su samu sauran kujerun majalisar.

Bisa sakamakon zaben, yawan kuri'un da jam'iyyar ANC ta samu a wannan karo bai zarce da yawansu na karon da ya gabata ba, kana yawan kuri'un da jam'iyyar DA shi ma ya ragu da kashi 1.5 cikin dari, amma yawan kuri'un da jam'iyyar EFF ya karu sosai.

Yawan masu jefa kuri'un zaben da aka yi rajista a wannan karo ya kai miliyan 26 da dubu 700, kashi 65 cikin dari na adadin sun jefa kuri'unsu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China