A yayin ganawar tasu, Song Tao ya nuna yabo matuka kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma jam'iyyun biyu, ya ce, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasar Afirka ta Kudu, domin aiwatar da ra'ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma kansu, da kuma gudanar da sakamakon da aka cimma yadda ya kamata, a yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing, da kuma taron ganawar shugabannin kasashen BRICS a birnin Johannesburg. Sa'an nan kuma, ya kamata a zurfafa mu'amalar dake tsakanin jam'iyyun biyu, ta yadda za a karfafa dunkulewar kasashen Sin da Afirka bai daya.
A nasa bangaren, shugaba Ramaphosa ya ce, yana son ci gaba da karfafa dangantakar dake tsakanin jam'iyyun ANC da JKS, domin kiyaye moriyar kasashe masu tasowa cikin hadin gwiwa, da kuma nuna adawa ga tsarin kasuwanci na bin ra'ayin radin kai. Kuma yana fatan za a kara hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasarsa bisa fannoni da dama domin tallafawa al'ummomin kasashen biyu. (Maryam)