Sashen nazarin kimiya da fasahar kere-kere na kasar wanda ya sanar da hakan, ya ce, jiya Alhamis wata rana ce mai tarihi ga kasar Afirka ta Kudu, bayan da kasar ta yi nasarar harba tauraron dan-Adam na zamani samfurin ZACube-2.
An dai harba tauraron dan-Adam na ZACube-2 ne da misalin karfe 4 da miti 7 na safe daga tashar harba tauraron dan-Adam ta Vostochny na kasar Rasha ta hanyar amfani da nau'urar Soyuz Kanopus na kasar ta Rasha.
Shi dai tauraron dan-Adam na ZACube-2 wanda ya bar doron duniya tare da wasu kananan taurarin dan-Adam daga kasashen Amurka da Japan da Spnaiya da Jamus, zai rika sa-ido ne kan aukuwar bala'u daga indallahi da wadanda bil-Adam ke haddasawa da sauran matakai na gaggawa.(Ibrahim Yaya)