Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi kira yau a yayin bikin bude taron baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa a nan Beijing cewa, ba za a iya tinkarar batutuwan sauyin yanayi, gurbatar teku, kiyaye halittu da sauran batutuwan muhalli da ake fuskanta a duniya, da kuma tabbatar da ajandar MDD ta samun ci gaba mai dorewa a shekarar 2030 ba, sai kasashen duniya sun hada kansu sosai.
Ya kara da cewa, kafa duniya mai kyan gani, buri ne na 'yan Adam baki daya. Yayin da ake daidaita kalubalen muhalli, babu wata kasa da za ta kare kanta kadai, ba tare da 'yan Adam sun hada kansu ba. (Tasallah)