Direktan cibiyar nazarin harkokin Sin ta kasar Nijeriya Charles Onunaiju ya bayyana cewa, matakan bude kofa ga kasashen waje da Sin take dauka sun amfanawa duniya, domin dukkan duniya na morar fasahohin samun ci gaba na kasar Sin. Wannan ya shaida cewa, Sin ta yi imani ga makomar bunka kanta, kana tana samar da gudummawa wajen shimfida zaman lafiya da na karko da samun ci gaba a duniya ta hanyar yin mu'amala da kasa da kasa.
A nasa bangaren, shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi ya bayyana cewa, bangarori daban daban masu shiga aikin raya shawarar "ziri daya da hanya daya" sun kyautata hanyoyin yin hadin gwiwa da kuma more fasahohin samun bunkasuwa tare. Ya ce tun daga hadin gwiwa da tsara shirye-shirye a gun taron kolin BRF karo na farko, har zuwa yanzu mahalartar taron sun yi taron da kyautata ayyukansu, wannan ya shaida cewa, an fara aiwatar da ayyukan bisa shirye-shiryen da suka tsara, da yin kokarin cimma burinsu.
Babbar manazarciya ta cibiyar nazarin harkokin yankin kudancin Afirka wato SARDC Madam Phyllis Johnson tana ganin cewa, a cikin jawabin shugaba Xi Jinping, tunanin raya kasa ta bude kofa da kiyaye muhalli da yaki da cin hanci da rashawa na da babbar ma'ana ga ci gaban kasashen Afirka. Ta ce ana kokarin kafa yankin ciniki cikin 'yanci a Afirka, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Afirka da Sin zai taimakwa raya yankin. Ta ce ya kamata kasashen Afirka su kara raya kansu, da hada manufofin raya kasa da aikin raya shawarar "ziri daya da hanya daya". (Zainab)