Game da wannan batu, Xi Jinping ya gabatar da shawarwari uku, na farko, ana fatan bangarori daban daban za su yi kokari tare da kyautata aikin hadin gwiwa don raya shawarar "ziri daya da hanya daya" mai kyautatuwa. Ya ce ya kamata a goyi bayan shigar da ajendar samun ci gaba mai dorewa ta MDD da ake son cimma zuwa shekarar 2030 cikin aikin raya shawarar "ziri daya da hanya daya", da sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kuma kiyaye muhalli bisa ka'idoji da ma'aunin da kasa da kasa suka amince, ta yadda kasa da kasa za su samu moriya daga cikin aikin da samun ci gaba tare. Na biyu, yana fatan za a tabbatar da ayyukan hadin gwiwa mafi muhimmanci, da kara yin mu'amala da hadin gwiwa a dukkan fannoni. Ya ce ya kamata a sa kaimi ga raya ayyukan more rayuwa, da hadin gwiwar dake tsakanin harkoki, da bunkasuwar tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a. Shawara ta uku da ya bayar, ita ce bangarori daban daban za su raya tsarin hadin gwiwa, da kafa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakaninsu. Shugaba Xi ya ce ya kamata a sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya mai bude kofa, da kin amincewa da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, da ci gaba da hada shawarar "ziri daya da hanya daya" da manufofin raya kasashe da yankuna, don samun moriyar juna. (Zainab)