Ministar kudi na kasar, Zainab Ahmed wadda ke halartar taro na 2 na hadin gwiwar kasa da kasa karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya a nan birnin Beijing, ita ce ta bayyana haka yau, a wata hira da ta yi da sashen Hausa na rediyon CRI.
Zainab Ahmed ta ce wannan zargin ba shi da tushe bare makama. Inda ta ce wajibi ne kan kowacce kasa dake neman aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa ta nemi bashi, don haka suke neman bashi daga wajen kasar Sin, la'akari da cewa nata na da rangwamen kudin ruwa da saukin biya.
Ta kara da cewa a tsarin bada bashi, dole sai an duba karfin kasa na iya biya kafin a bata, don haka babu ta yadda za a yi a ce kasar Sin na bada kudaden ne domin dana tarkon bashi.
Ta ce a matsayinsu na kasashe masu tasowa, su na bukatar taimako daga manyan kasashe irin kasar Sin, kuma dangantakar kasashen biyu na moriyar juna ne, domin kamfanonin kasar Sin da ke aiki a kasar na daukar ma'aikata 'yan kasar tare da koya musu aiki.
Zainab Ahmed ta ce makasudin zuwan su shi ne, kara tattaunawa da cimma yarjeniyoyi da kasar Sin domin Babban Bankin kasar ya ba su rancen gudanar da manyan ayyukan more rayuwa.
Ministar ta ce ayyukan da suke son gudanarwa bisa hadin gwiwar kasar Sin sun hada da shimfida layin dogon da ya tashi daga Ibadan zuwa Kano da kammala gyaran filayen jiragen sama 4 na biranen Abuja da Lagos da Fatakwal da kuma Kano, da aikin madatsar ruwan mambila dake jihar Plateau da sauransu, wadanda bayan kammalawa, za su samar da dimbin alfanu ga kasar. (Fa'iza Msutapha)