A cikin sakon, Xi Jinping ya ce, sake zaben Kim Jong Un a matsayin shugaban hukumar, yayin zama na farko na majalisar koli ta al'ummar kasar karo na 14, ya nuna yadda shugaba Kim ya samu karbuwa da goyon baya daga Jam'iyyarsa da kuma al'ummar kasar, yana mai taya shi murna tare da yi masa fatan alkhairi.
Shugaban na kasar Sin ya kara da cewa, a shirye yake ya yi aiki da shugaba Kim Jung Un ta hanyar amfani da cikar kasashensu shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya, domin kara ingnata dangantakarsu ta yadda kasashen 2 da al'ummominsu, za su samu karin moriya. (Fa'iza Mustapha)