in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu tsohon Alkalin Alkalan Nijeriya da laifin kin bayyana kadadorin da ya mallaka
2019-04-19 09:33:22 cri
An samu dakataccen Alkalin Alkalan Nijeriya Walter Onnoghen, da laifin kin bayyana kadarorin da ya mallaka, inda aka haramta masa rike wani mukamin gwamnati tsawon shekaru 10.

A hukuncin da shugaban kotun da'ar ma'aikataka Danladi Umar ya yanke a jiya Alhamis, ya ce Walter Onnoghen ya take dokar da'ar ma'aikata, don haka an tube shi daga mukaminsa na Alkalin Alkalan Nijeriya.

Hukuncin na nufin an samu Walter Onnoghen da laifin kin bayyana asalin kadarorin da ya mallaka a lokacin da ya kama aiki.

Kotun da'ar ma'aikatar, ta kuma bada umarnin kwace dukkan kudaden dake cikin asusun da tsohon Alkalin Alkalan ya gaza bayyanawa, inda za a mika su ga gwamnatin tarayyar kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China