in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyoyin ma'aikatan bangaren man fetur a Nijeriya sun musanta matsalar karancin mai a kasar
2019-04-14 17:00:06 cri
Kungiyoyin ma'aikatan bangaren man fetur a Nijeriya, sun musanta rahotannin dake cewa, ana fuskantar karancin man fetur a wasu sassa na kasar mai arzikin man fetur, inda suka yi kira ga jama'ar su daina hanzarin sayen man fetur din da diesel.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na kasar sun ruwaito cewa, ana fama da karancin mai a wasu biranen kasar, saboda zargin da ake cewa wasu dilallan man sun ki dakonsa daga rumbunan dake adana shi.

Kungiyar dillalan man fetur ta kasar IPMAN da kungiyar ma'aikatan bangaren hakar mai da iskar gas, sun bukaci 'yan Nijeriya su daina tada hankalinsu kan karancin man fetur, domin akwai isasshe.

Kungiyoyin sun yi tsokaci ne a jiya Asabar, a mabanbantan lokuta a birnin Lagos.

Kungiyar IPMAN ta tabbatar da cewa, yanzu haka, jiragen ruwa na dakon mai 6 da kamfanin mai na kasar NNPC ya oda, na sauke man da suke dauke da shi, suna masu tabbatar da cewa kamfanin na da isasshen albarkatun mai.

A nasa bangaren, kamfanin NNPC ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, yana da sama da lita biliyan 1 na mai a ajiye, inda yake kuma da karin wasu kwantainonin mai 48 dauke da lita miliyan 50 da aka ware ga watan Afrilu kadai.

Wani jami'in kungiyar IPMAN Clement Isong, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, suna aiki da kamfanin NNPC domin tabbatar da an dai na samun layukan a giajen mai. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China