Cikin wata sanarwa da aka fitar, Muhammadu Buhari, ya sabunta alkawarinsa yayin da ake cika shekaru 5 da sace 'yan matan.
Kimanin 'yan mata 210, na sakandaren garin Chibok na jihar Borno ne aka sace a ranar 14 ga watan Afrilun 2014, inda daga bisani aka saki 107 daga cikinsu, biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin da kungiyar.
A wa'adin mulkinsa na farko a shekarar 2015, Shugaban ya yi wa iyayen 'yan matan alkawarin tabbatar da sada su da 'ya'yansu.
Shugaban ya bayyana cewa, wannan alkawarin ne ya sa al'ummar garin Chibok su ka sake zabarsa a zaben da aka yi cikin watan Faburairu.
Ya ce duk da kawo yanzu gwamnatinsa ta yi nasarar karbo 'yan mata 107, ba za ta gajiya ba, har sai ta sada ragowar 'yan matan da iyayensu, yana mai tabbatar da cewa har yanzu gwamnatinsa na aiki kan batun. (Fa'iza Mustapha)