Adam Elhiraika, ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa, yana mai cewa cimma muradun ci gaba mai dorewa, da muradun Afirka na ci gaba nan da shekaru 50 masu zuwa wato zuwa shekarar 2063, ba za su kai ga nasara ba, har sai an samar da tsare tsare na inganta da hade sassan tattalin arziki.
Jami'in na hukumar ECA ya kara da cewa, nahiyar Afirka na matukar bukatar manufofi na fadada da sauya tsarin masana'antun ta, da kuma inganta sha'anin hada hadar kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar, musamman karkashin tsarin yarjejeniyar gudanar da cinikayya cikin 'yanci ta AfCFTA.
Elhiraika, ya kuma jaddada bukatar rage tasirin hadurra da tattalin arzikin duniya ke haifarwa ga kasashen nahiyar, kamar tarnaki ga kasuwannin kasa da kasa, da yawan sauyawar farashin kudaden musaya, da zirarewar kudade, da hauhawar farashin hajoji.(Saminu Alhassan)