Gwamnatin kasar ta ce tana hada hannu da hukumar kula da kaura ta duniya IOM da sauran hukumomin kasa da kasa abokan hulda, wajen samar da manufar kasar ta farko game da batun kaura.
Wata sanarwa da IOM ta fitar biyo bayan wata ganawa da aka yi a Juba, ta ruwaito mataimakin ministan harkokin cikin gidan kasar Riaw Choul na cewa, gwamnati ta kuduri aniyar rungumar wannan manufar domin za ta kai kasar ga samar da kyakkyawan yanayin ga masu zuba jari na kasashen waje da tabbatar da masu kaura sun kiyaye dokokin kasar domin kariyarsu.
A cewar hukumar IOM, da zarar an kammala daftarin, za a mika shi ga majalisar ministoci domin nazartarsa tare da amincewa da shi.
A cewar rahoton IOM, a shekarar 2017, Sudan ta Kudu ta bada mafaka ga masu kaura 845,000, galibinsu daga yankunan gabashi da kahon Afrika. (Fa'iza Mustapha)