in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Sabon fada ya tilastawa mutane 5000 tserewa a Sudan ta kudu
2019-02-13 11:11:40 cri
Hukumar kula da 'yan gudun hijirar MDD (UNHCR) ta bayyana jiya Talata, cewar kimanin mutane 5000 ne a Sudan ta kudu suka tserewa sabon fada da ya barke a kasar, inda suka tsallaka zuwa jihar Central Equatorial kana daga bisani suka arce zuwa jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC).

Babban kwamishinan hukumar UNHCR ya ce, 'yan gudun hijirar sun isa wasu kauyuka da dama dake kusa da kan iyakar garin Ingbokolo, a arewa maso gabashin lardin Ituri dake DRC, bayan da suka tserewa sabon fadan wanda ya fara tun a ranar 19 ga watan Janairu tsakanin sojoji da daya daga cikin kungiyoyin 'yan tawayen kasar mai suna NAS.

Bisa sanarwar hukumar ta UNHCR, an ce, a cikin 'yan kwanakin da suka gabata dubban mutanen dake cikin matsanancin hali sun tsallaka kan iyakokin kasar domin gujewa fada da cin zarafin da ake yiwa fararen hula. Akwai wasu rahotanni dake cewa akwai wasu karin mutanen kimanin 8000 wadanda rikici ya raba su da gidajensu dake zaune a wasu sassa a cikin kasar ta Sudan ta kudu, a kan iyakar garin Yei.

UNHCR ta nanata yin kira ga dukkan bangarorin dake rikici da juna da su dauki dukkan matakai na tabbatar da tsaron lafiyar fararen hula da kuma ba su 'yancin walwala, kana su samar musu hanyoyin da za su bi don ficewa daga yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China