Kuol Manyang Juuk, ministan tsaro da kula da harkokin sojojin da suka yi ritaya na kasar, ya ce sashen baiwa yara kariya na hukumar sojoji ta kasar yana ci gaba da aiki babu kakkautawa tare da kwamandojin sojojin kasar domin tsame kananan yara daga ayyukan yaki.
Ya kara da cewa, gwamnatin kasar ta bayar da umarni ga dukkan manyan janar janar na sojojin kasar da su bada hadin kai ga hukumomin MDD da abin ya shafa domin tabbatar da ganin an dakile shigar da kananan yara ayyukan soji, yana mai cewa, dakarun wanzar da tsaron jama'ar kasar Sudan ta kudu (SSPDF) ta horar da wasu jami'anta masu baiwa yara kariya sama da 100 a yunkurin da take na inganta aikin soji.
"Wannan daya ne daga cikin matakan da ake dauka domin tsabtace hanyoyin ingancin aikin soji. Ba mu da wani zabin da ya wuce samar da ingantacciyar rundunar sojoji, rundunar sojin da za ta kare hakkin dan adam da dukiyoyin al'ummar kasa," Juuk ya bayyana hakan a Juba.(Ahmad Fagam)