Yayin da yake kammala ziyarar yini 3 a Sudan ta Kudu a jiya, Mataimakin Sakatare Janar na MDD kan ayyukan wanzar da zaman lafiya Jean Pierre Lacroix, ya bayyanawa manema labarai a Juba cewa, sun samu kwarin gwiwa saboda ci gaban da aka samu daga bangarorin masu rikici, musammam na tsagaita bude wuta yayin da rikici ya barke a bayan- bayan nan a kudu maso yammacin jihar Yei River da jihar Unity
Ita kuwa babbar daraktar hukumar kula da harkokin mata ta MDD Phumzile Mlambo-Ngcuka, cewa ta yi, matan Sudan ta Kudu na son a yi aiki da su a fannin sake fasalin tsarin tsaro, wanda ya kunshi ba su dama ta taka rawa tare da bada gudunmuwa wajen tabbatar da tsaron kasar wanda zai haifar da raguwar ayyukan soji.
A nasa bangaren, Smail Chergui na kwamitin tsaro na AU, ya ce kowa da kowa musammam ma fararen hula, na kara fata da bukatar aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin shugaban kasar Salva Kiir da shugaban 'yan tawaye Riek Machar da sauran bangarori 'yan adawa. (Fa'iza Mustapha)