Shugaba Ramaphosa ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a birnin Cape Town, yayin da yake jawabi gaban mahalarta taro na 8, wanda cibiyar wanzar da zaman lafiya ta Desmond Tutu ta shirya. Yayin taron na shekara shekara, shugaban Afirka ta kudun ya ce, "A matsayin mu na 'yan Afirka ta kudu, mun san cewa, ba rashin yaki ne kadai zaman lafiya ba, a'a har ma da kakkabe rashin adalci".
Ramaphosa ya kuma yi amfani da jawabin na sa, wajen jaddada goyon baya ga sauye sauyen da ake gudanarwa, game da sake raba filaye ba tare da biyan kudin diyya ba, batun da ke ci gaba da yamutsa hazo a tsakanin 'yan kasa.
Ya ce Afirka ta kudu ba za ta kai ga samun cikakken zaman lafiya da walwala ba, har sai an cimma nasarar raba arzikin kasar daidai wa daida tsakanin al'ummun ta, kana an raba filayen kasar tsakanin wadanda suka yi aikin kyautata su.
Daga nan sai ya soki matakin raba bakaken fata da filayen su, yana mai cewa hakan na karya kashin bayan duk wani yunkuri da ake yi, na wanzar da zaman lafiya mai dorewa.
Ya kuma yi suka game da yadda masu nuna wariyar launin fata, suka rika raba bakaken fata, da wadanda asalinsu ba farare ba, da 'yan asalin Indiya da filaye, da dukiyoyin su, tare da cin zarafin su. (Saminu Alhassan)