A cewar Wang Annan, jami'i a ma'aikatar albarkatun ruwa na kasar, tun daga shekarar 2014 ake aiwatar da wasu ayyukan adana ruwa 132, inda suka lakume fiye da yuan triliyan 1, kwatankwacin dala biliyan 146.
Ya ce wadannan ayyukan sun inganta samar da ci gaba a cikin yankuna da kuma aikin kawar da talauci, la'akari da yadda kaso 75 na ayyukan 132 suka kasance a yankunan tsakiya da yammacin kasar, yayin da kaso 56 suka kasance a wuraren dake fama da talauci.
Ayyukan na daga cikin shirin kasar da aka sanar a shekarar 2014, da nufin gina wuraren adana ruwa 172 ya zuwa shekarar 2020.
Tuni sama a kaso 80 na ayyukan 172 za su fara gudana ya zuwa karshen 2019, kuma babban aiki irin wannan da za a yi a 2019 shi ne na yankin kogin Pearl. (Fa'iza Mustapha)