Kasar Sin tana da filayen jirgin sama 37 da kowanensu ya yi jigilar fasinjoji sama da miliyan 10 a duk shekara
Filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa na Hefei Xinqiao dake gabashin kasar Sin a lardin Anhui, ya shiga cikin jerin filayen jiragen sama da hukumomin kasar suka amince da su wadanda ke iya jigilar fasinjoji sama da miliyan 10 a duk shekara ya zuwa karshen watan Nuwamba, in ji hukumar jiragen saman.
Filin jirgin saman ya kasance na 37 a kasar Sin wanda ya kai matsayi na yin jigilar fasinjoji sama da miliyan 10 a duk shekara, in ji hukumar kula da filayen jiragen saman
Ya zuwa karshen watan Nuwamba, kasar Sin ta samu karin jiragen sama 5 wadanda suka shiga cikin jerin filayen jiragen sama dake iya jigilar fasinjoji miliyan 10 a tsawon wannan shekarar. (Ahmad Fagam)