A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, wakiliyar musamman mai kula da tsaro da zaman lafiyar mata ta kungiyar AU, Mme Bineta Diop, ta sanar da cewa, rahotannin baya bayan nan sun nuna cewa kimanin mata da 'yan mata 150 ne aka yi wa fyade da kuma dukansu a garin Bentiu dake Sudan ta kudu.
Diop, ta bukaci masu ruwa da tsaki a matakan shiyya, nahiya da matakan kasa da kasa da su kai daukin gaggawa domin ceto matan da aka ci zarafinsu ta hanyar lalata a Sudan ta kudun.
Tun bayan barkewar yakin basasa a watan Disambar shekarar 2013 a Sudan ta kudu, wanda aka samu ruruta wutar rikicin sakamakon banbancin kabila da nuna son zuciya, an yi kiyasin dubban mutane ne rikicin ya yi sanadiyyar salwantar rayukansu, kana wasu mutanen kusan miliyan 4 tashin hankalin ya raba su da matsugunansu. (Ahmad Fagam)