Masu fafutukar sun hada da masana daga bangaren makarantun ilmi da kungiyoyin fararen hula inda suka lashi takobin shirya gangamin nuna adawa da tsarin al'adun da nufin kawo karshen nuna bambancin jinsi da cin zarafin mata da 'yan mata a duk fadin kasar wanda ya samo asalin tun bayan barkewar yakin basasar kasar cikin shekaru 5 da suka gabata.
Ayak Chol Deng Alaak, wata mai rajin kare hakkin mata ta bayyana cewa, sabon gangamin da suka shirya zai kawo karshen mumunan al'adun kasar kamar auren wuri wanda ke tauye mata wajen hana su samun damammaki a fannonin rayuwa. (Ahmad Fagam)