Sakatare Janar na hukumar kula da zuba jari ta kasar, Abraham Maliet Mamer, ya shaidawa manema labarai a birnin Juba cewa, kofar kasar a bude take, kuma a shirye take, ta karbi jarin da zai farfado da tattalin arzikinta.
Ya ce kofofin kasar sun dade a rufe, yanzu kuma lokaci ya yi na magana da babbar murya kuma a bayyane cewa, kasar ta shirya karbar jari.
Sudan ta Kudu dai ta dogara ne da samar da man fetur, wanda ke samar da kaso 98 na kudaden da take kashewa, kuma a baya bayan nan ne ta sanar da yunkurinta na bunkasa samar da man da ya gamu da tsaiko biyo bayan rikice-rikice, al'amarin da ya sa yawan man da kasar ke samarwa ya ragu zuwa kasa da ganga 165,000 a kowacce rana, daga ganga 350,000 a shekarar 2012.
Sudan ta Kudu ta shirya karbar taron zuba jari kan man fetur da iskar gas karo na 2, a ranekun 21 da 22 na watan nan a birnin Juba. An yi taron na farko ne a watan Oktoban bara. (Fa'iza Mustapha)