Gwamnan babban bankin kasar Sin Yi Gang, ya ce yanayin darajar kasuwar hannayen jari na kasar ya yi kasa a tarihi, idan aka kwatanta da karfi da ci gaban tattalin arzikin kasar.
Yi Gang ya bayyana hake ne lokacin da yake ganawa da manema labarai game da darajar kasuwar hannayen jarin kasar inda ya ce babban bankin zai ci gaba da tafiyar da kudaden ajiyarsa bisa yanayi mai karko domin inganta yanyain tattalin arziki da samar da kyakkyawan yanayin hada-hadar kudi. (Fa'iza Mustapha)