Kungiyar ba da agajin jin kai ta "Save the Children" ce ta fidda wannan alkaluma, tana mai cewa akwai yara kanana kimanin 20,000, wadanda mai yiwuwa ne su rasa rayukan su, nan da karshen shekarar bana, sakamakon tsananin yunwa dake addabar kasar.
Kungiyar ta ce kusan rabin daukacin al'ummar kasar Sudan ta kudu na fuskantar tsananin yunwa. (Saminu Alhassan)