Bisa labarin da ma'aikatar harkokin kasuwanci ta fidda a yau Alhamis, an ce, daga watan Janairu zuwa watan Satumba na shekarar bana, yawan jarin da kasar Sin ta samu daga kasashen ketare ya kai RMB biliyan 636.7, adadin da ya karu da kashi 2.9 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. A sa'i daya kuma, adadin sabbin kamfanonin da aka kafa a kasar Sin, wadanda suka samun jari daga 'yan kasuwar ketare ya karu da kashi 95.1 bisa dari.
Kakakin ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana cewa, cikin farkon watanni 9 na shekarar bana, adadin jarin ketare da kasar Sin ta yi amfani da su ya karu cikin madaidaicin yanayi, kuma adadin kafuwar sabin kamfanoni a kasar Sin shi ma ya karu cikin sauri. (Maryam)