A kuri'ar da aka kada wanda ta samu amincewar dukkan mambobin kwamitin MDDr kan kudirin doka mai lamba 2438, kwamitin MDDr ko kuma UNISFA, zai tsawaita wa'adin aikin wanzar da zaman lafiyar zuwa ranar 15 ga watan Afrilun 2019 a yankin na Abyei da ake takaddama kansa tsakanin Sudan da Sudan ta kudu, idan har kasashen biyu suka cigaba da jan kafa wajen gaza samar da gagarumin cigaba na warware rikicin kan iyakokin nasu.
A cewar daftarin, ana saran Sudan da Sudan ta kudu zasu dauki wasu matakai guda 7 nan da watanni 6 masu zuwa, game da batun shata kan iyakokin nasu, wanda ya kunshi bada 'yancin zirga-zirgar jami'an kiyaye zaman lafiya na UNISFA, da fara aiwatar da tantance sassa 10 na iyakokin kasashen biyu don bada damar zirga zirgar alummominsu, da kuma gudanar da tattaunawa a kalla sau biyu na hukumar hadin gwiwa mai kula da kan iyakokin kasashen da kuma kwamitin shata kan iyakokin kasashen biyu. (Ahmad Fagam)