Wata sanarwa da rundunar sojan kasar Sin ta fitar ta bayyana cewa, mataimakin shugaban ofishin kula da harkokin hadin gwiwar sojojin kasa da kasa na rundunar sojan kasar Sin Huang Xueping ya gayyaci mai rikon mukamin jami'in kula da harkokin soja dake ofishin jakadancin Amurka a nan kasar Sin kan wannan batu.
A ranar Alhamis ne ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta sanar da cewa, za ta kakabawa sashen kula da makaman sojojin kasar Sin da ma darektan sashen takunkumi, wai tana zargin cewa, kasar Sin ta sabawa dokokin alakar harkokin soja na kasar Amurka.
Sai dai Huang ya ce, hadin gwiwar soja tsakanin kasashen Sin da Rasha kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada. Haka kuma kasar Sin tana adawa da matakin Amurka kuma ba za ta taba amincewa da shi ba. A hannu guda kuma kasar Sin za ta hanzarta dawo da kwamandan ruwan kasar Shen Jinlong da yanzu haka yake halartar taron karawa juna sani kan inganta dabarun sojojin ruwa na kasa da kasa karo 23 dake gudana a kasar ta Amurka zuwa gida, ta kuma dakatar da ganawa game da harkokin sadarwa na hadin gwiwa tsakanin ma'aikatan sassan biyu da aka shirya gudanarwa tsakanin ranakun 25-27 ga watan Satumba a birnin Beijing.
A wani labarin kuma, mataimamkin ministan harkokin wajen kasar Sin Zheng Zeguang ya gayyaci jakadan Amurka dake Sin Terry Branstad tare da gabatar da koke da rashin kin amincewa game da takunkumin da Amurka ta kakabawa hukumar kula da harkokin sojan kasar Sin, inda ya bukaci daukar mataki bisa doka.
Zheng ya yi nuni da cewa, bangaren Amurka ya dauki wannan ne, saboda alakar soja dake tsakanin Sin da Rasha, wanda ya ce hakan ya saba dokokin kasa da kasa, kuma irin wannan mataki ba shi da tsari ko kadan.
Ya ce, kasar Amurka ba ta da ikon tsoma baki kan alakar soja dake tsakanin Sin da Rasha, wanda jami'in ya ce tana gudana yadda kamata.
Minista Zheng ya ce, bangaren kasar Sin zai dauki matakan da suka dace domin kare muradun kasarsa. Don haka Sin na kira ga bangaren Amurka da ya hanzarta gyara kura-kuransa, sannan ya janye takunkumim da ya kakaba mata, idan ba haka ba, duk abin da ya biyo baya, Amurkar ce ta janyowa kanta. (Ibrahim)