Gao Feng ya ce karuwa ko raguwar gibin cinikayya, na da nasaba ne da yanayin kasuwa. Jami'in wanda ya bayyana hakan yayin wani taron ganawa da 'yan jarida a jiya Alhamis, ya amsa wata tambaya dake da nasaba da batun karin harajin na Amurka.
Wasu alkaluman kididdiga na hukumar kwastam ta Sin sun nuna cewa, cikin watanni 8 kacal, ranar cinikayya tsakanin Sin da Amurka ya karu da kaso 7.7 bisa dari, adadin da ya tasarwa dalar Amurka biliyan 181, yayin da kuma yawan hajojin da ake shigarwa Amurka daga Sin suka karu da kaso 6.5 bisa dari.
A cewar Mr. Gao, karuwar yawan hajojin na da nasaba da karuwar bukatar su a kasuwannin Amurka, da ma karuwar sayayya daga manyan 'yan kasuwa, wadanda ke ganin mai yiwuwa karin harajin na Amurka, ya tsawwala farashin kayan da suke saya daga Sin.
Jami'in ya ce babban dalilin faruwar gibin cinikayyar Amurka, shi ne karancin kudaden ajiyar kasar, da matsayin dalar Amurka a jerin kudaden ajiyar kasa da kasa, da kuma tsoma hannun gwamnatin kasar a harkokin fitar da kayayyaki zuwa Sin. (Saminu)